12 Yuli 2016 - 17:40
Iraki : Dan Kunar bakin Wake Ya Kashe Mutane 7

Rahotanni daga Iraki na cewa wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane bakwai a Bagadaza babban birnin kasar.

Bayanai daga kasar sun ce dan kunar bakin waken da yayi jigida da boma-bamai ya tarwatsa kan sa da motar da ya ke ciki a tsakiyar kasuwar gwari dake arewa maso gabashin kasar a wannan Talata.

ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu akwai wasu mutane 29 da suka jikkata a cewar rahotanni.

Har kawo lokacin fasara wadanan labaren babu wata kungiya data dau alhakin kai wannan harin, saidai sau tarin yawa akan danganta ire-iren wadanan ayyukan ta'adi ga kungiyar yan ta'ada mai kafirta musulmai da aka fi sani da Da'esh ko kuma (IS)